عربيEnglish

The Noble Qur'an Encyclopedia

Towards providing reliable exegeses and translations of the meanings of the Noble Qur'an in the world languages

Banning [At-Tahrim] - Hausa translation - Abu Bakr Jomy

Surah Banning [At-Tahrim] Ayah 12 Location Madanah Number 66

Kuma a sã'ilin da Annabi ya asirta wani lãbãri zuwa ga sãshen mãtansa, to, a lõkacin da ta bã da lãbari da shi. Kuma Allah Ya bayyana shi a gare shi, ya sanar da sãshensa kuma ya kau da kai daga wani sãshe. To, a lõkacin da ya bã ta lãbãri da shi, ta ce: "Wãne ne ya gaya maka wannan?" Ya ce: "Masani, Mai labartãwa, Ya gaya mini."

Kuma Allah Ya buga wani misãli dõmin waɗanda suka yi ĩmãni; matar Fir'auna,[1] sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurin Ka a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutãnen nan azzãlumai."